Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a wani turmutsutsu yayin da suke kokarin karbar Zakka da wani dan kasuwa – AYM Shafa ke rabawa a jihar Bauchi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, turmutsutsin ya faru ne a ranar Lahadi a ofishin Shafa Holdings da ke kan titin Jos a cikin babban birnin Bauchi.
Talakawa da mabukata, wadanda shari’ar Musulunci ta bukaci a baiwa zakka, sun taru ne a harabar ofishin tun da safe suna jiran zakkar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce, kimanin mutane hudu ne suka rasa rayukansu a turmutsutsun.
Leave a Reply